Connect with us

Hausa

Nnamdi Kanu na amfani da Tuwita wajen ta da rikici a Najeriya – Lai Mohammed

Published

on

Lai Mohammed

Asalin hoton, Getty Images

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu na Najeriya Lai Mohammed, ya ce Nnamdi Kanu jagoran ƙungiyar IPOB mai fafutukar ɓallewa daga Najeriya yana amfani da Tuwita wajen yaɗa farfagandarsa don kawo rashin zaman lafiya a ƙasar.

Mista Mohammed ya ce Nnamdin Kanu yana yawan amfani da shafin wajen tunzura mabiyansa su kai hare-hare gine-ginen gwamnati.

Ministan ya bayyana haka ne a zantawarsa da shirin BBC Focus on Africa a ranar Litinin.

Lokacin da aka tambaye shi ko za a tuhumi Mista Adeboye saboda amfani da Twitter, duk da hujjar da ya bayar kan amfani da dandalin, sai ya ce babban lauyan gwamnatin ƙasar Abubakar Malami shi zai tabbatar da ganin an hukunta duk wanda ya taka dokar hana amfani da Tuwita a kasar, ciki har da Fasto Enoch Adeboye, wanda yayi wani rubutu a shafin bayan hani da gwamnati ta yi.

Mista Lai ya jaddada cewa ci gaba da amfani da Tuwita a Najeriya zai iya kawo rarrabuwar kan ‘yan kasar.

Ga fassarar hirar da ya yi da Bola Mosuro ta shashen BBC Focus On Africa, wadda Zaradden Lawal ya fassara.

Tambaya: Me ya sa gwamnati ta dakatar da amfani da Tuwita?

Amsa: Gwamnati ta dakatar da aikace-aikacen Tuwita a Najeriya saboda amfanin da ake yi da dandalin babu ƙaƙƙautawa wajen yin zagon ƙasa ga ci gaba da kasancewar Najeriya wuri guda.

Sannan kuma gwamnati ta umarci hukumar kula da kafafen yada labarai da ta fara shirye-shiryen ba da lasisi ga kafafen yaɗa labarai na intanet.

Saboda kamar yaddda na ce ana amfani da Tuwita wajen raba kawunan ‘yan Najeriya.

Tambaya: Taƙamaimai me kake nufi? Ta yaya idan jama’a idan sun yi wani tsokaci a kan wahalhalun da Najeriya ke ciki a Tuwita zai haifar da rarrabuwar kan ‘yan kasar?

Amsa: Wato idan kika duba kungiyar IPOB musamman Nnamdi Kanu, yana ƙoƙarin wargaza kasar, wanda yake zaune a wajen Najeriya, inda yake umartar mambobinsa suna kai wa gine-ginen gwamnati kamar ofisoshin ‘yan sanda da sojoji da gidan yari da kuma ofisoshin hukumar zabe hare-hare, ta hanyar amfani da shafin Tuwita ba tare da an ɗauki wani mataki ba.

Tambaya: Amma wani zai iya cewa daukar matakin a kansu tamkar ƙoƙari ne na tauye wa jama’a musamman wadanda ba su yi wa gwamnati komai ba haƙƙinsu na shiga intanet don samun bayanai?

Amsa: Idan Najeriya ta hargitse aka samu rashin tsaro a ko ina to kin ga babu wanda ke da wani ƴanci ko haƙƙi.

Tambaya: To amma mai girma minista ai dama akwai matsalar rashin tsaron a sassan kasar.

Amsa: Eh haka ne. To shi kenan kuma sai ya kamata a yi amfani da Tuwita a ƙara rura matsalar tsaron?

Tambaya: Shin wai ta yaya za ku hukunta wadanda suka bujirewa umarnin da kuka bayar da cewa kar a yi amfani da Tuwita, saboda mun ga Fasto Enoch Adeboye ya yi rubutu a Tuwita inda ya ce haƙƙinsa ne na ɗan adam ya yi hakan, shin za ku hukunta shi kenan?

Amsa: Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati yayi bayani dalla-dalla cewa duk wanda ya taka wannan doka to za’a hukunta shi.

Wannan ba magana ba ce ta wani mutum guda. Ina ganin shi babban lauyan gwamnati shi ne zai ce ga wanda za a hukunta ko a’a.

Tambaya: Akwai wadanda suke ganin kuna ƙoƙarin amfani da damar daƙile aikace-aikacen kungiyar IPOB ne don kuna so ku taƙaita yadda ake amfani da shafukan sada zumunta?

Amsa: Eh gaskiya ne ko yaushe ina fafutukar ganin an tsaftacce yadda ake amfani da shafukan sada zumunta saboda illar da ke tattare da yada labaran ƙanzon kurege.

Kuma har yanzu ina kan wannan matsaya cewa lalle ya kamata a yi amfani da shafukan yadda ya kamata.

Karin labaran da za ku so

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending