Ƴan sanda na bincike kan mutuwar mutane uku ƴan gida ɗaya a Kwara

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, Victor Olaiya, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan mutuwar wasu ‘yan’uwa guda uku da suka mutu a cikin mota da ke tsaye a garin Ilorin  babban birnin jihar.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadi da ta gabata.

A cewar wani mazaunin unguwar, ’yan sandan sun kasa shiga ginin saboda kofar a kulle da kwaɗo take, kuma babu kowa a gidan.

Rahotanni sun nuna cewa daga bisani ‘yan sandan sun zarce zuwa gidan mahaifiyar marigayiyar da ke kan titin Taiwo Isale, Ilorin, inda take ta jimami bayan ta suma sakamakon mutuwar ‘ya’yanta a ranar Lahadi. 

Ƴan sandan sun tambayi uwar a kan  me ya sa ba ta kai rahoton lamarin a hukumance gare su ba.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]