Wani direban mota mai shekaru 21 daga jihar Gombe, Suleiman Rabiu, ya yi tattakin sama da kilomita 700 domin nuna yabonsa ga Hafsan Hafsoshin Tsaro, Janar Christopher Musa, saboda halaye da salon jagoranci.
Rabiu ya bar jihar Gombe ne a ranar 12 ga watan Fabrairu, ya isa Abuja ranar 28 ga Fabrairu, 2024, inda ya kwashe kwanaki 16 a hanya.
A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, Daraktan yada labarai na tsaro, Brig. Janar Tukur Gusau, ya ce salon shugabancin CDS ne ya zaburar da shi domin alaƙanta kansa da Shugaban Rundunar Sojin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Suleiman wanda ya bar jihar Gombe a ranar 12 ga Fabrairu, 2024, ya isa Abuja, a jiya 28 ga Fabrairu, 2024, bayan ya shafe kwanaki 16 a kan hanya, duk da rashin kyawun yanayi.”
Matashin ya ce ya hau hanya ya yi tafiyar ne don nuna godiyarsa ga kyawawan halaye da jagoranci na shugaban.
A cewarsa, tsaro na rayuka da dukiyoyi ya inganta sosai tun bayan hawansa mulki.”