Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko Haram a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Jakadan Qatar A Nijeriya Dr Ali Bn Ghanem Al-Hajari ne ya shaida wa Gwamna Babagana Umara Zulum hakan.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake aza harsashin ginin wata sabuwar makarantar firamare a jihar Bornon, wacce aka yi da nufin taimakon kokarin gwamnatin jihar na inganta ilimi.

More from this stream

Recomended