Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile Epo dake jihar.

Rikici ya ɓarke a kasuwar ranar Laraba bayan wani saɓani da aka samu kan wasan cacar Lotto har ta kai ga ɓata gari sun  ƙona shaguna da dama da kuma gidajen katako na kwanan mutane.

A cewar wasu majiyoyi wani mutumin arewa ne ya ci maƙudan kuɗi a cacar ta Lotto amma sai masu shagon cacar suka ƙi bashi duka kuɗin da ya ci abin ya haifar da rikici.

An tura tawagar jami’an tsaro ya zuwa kasuwar da safiyar ranar Alhamis.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Legas,Benjamin Hundeyin ya ce tuni al’amura suka ci gaba da gudana a kasuwar kamar yadda aka saba.

“Sama da mutane 50 da ake zargi aka kama kawo yanzu a yayin da gidajen katakon da suke kwana aka rushe su domin raba su da kasuwar,” a cewar Hundeyin..

Tuni kwamishinan ƴan sandan jihar, Adegoke Fayoade  ya bayar da umarnin gaggauta gurfanar da mutanen da aka kama a gaban kotu.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...