An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka’ida ba a kasuwar Karmo dake Abuja.

Mukhtar Galadima daraktan sashen dake kare birnin daga bunÆ™asa ba tare da tsari ba ya ce an fara rushe-rushen ne biyo bayan Æ™arewar wa’adin awanni 24 da aka bawa Æ´an kasuwar na su tashi daga wurin.

Galadima wanda ya samu wakilcin Garba Jibril mataimakin darakta dake lura da yankin Karmo da sauran wasu yankuna ya ce an sanar da dukkan mutanen da abun ya shafa inda ya Æ™ara da cewa anbi dukkanin wata ka’ida kafin a fara aikin.

“A fili yake Æ™arara mutane suna shafe a wanni kafin su wuce ta titin  musamman ranar da kasuwa take ci,” ya ce.

“Domin shawo kan wannan matsalar ministan Abuja Nyesom Wike ya bayar da umarnin rushe gine-gine da aka yi ba bisa ka’ida ba,” ya ce.

Galadima ya yi kira ga Æ´an kasuwar da abun ya shafa da su koma kasuwannin da aka samar .

More News

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...

Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus...

Kotu ta yanke wa É—ansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin...