Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da ya tashi daga Abuja-Kaduna a shekarar 2022.

Mai magana da yawun rundunar Olumiyiwa Adejobi shi ne ya bayyana haka a Kaduna ranar Alhamis lokacin da yake bayani kan ayyukan rundunar.

Adejobi ya ce sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ne ya kama Abdullahi wanda aka fi sani da Mande a ranar 12 ga watan Janairu.

Ya ce Abdullahi ya amsa cewa shi jagora ne na masu garkuwa da mutane da suka addabi hanyar Kaduna-Abuja.

A ranar 22 ga watan Maris ne na  shekarar 2022 wasu gungun ƴan bindiga suka kai harin kan jirgin ƙasar inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu suka kuma yi garkuwa da wasu mutane 61.

An sako mutanen daga baya rukuni-rukuni kuma a lokuta daban-daban inda aka sako rukunin ƙarshe bayan watanni 7 da harin.

Adejobi ya ƙara da cewa Mande na da hannu a sace ɗaliban Jami’ar Greenfield dake Kaduna.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...