EFCC ta kwato naira biliyan 60 cikin kwanaki 100

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Kasa Tu’annati, Mista Ola Olukoyede, ya ce a cikin kasa da kwanaki 100 da hawansa mulki, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta karbi korafe-korafe sama da 5,000 na zamba tare da kwato Naira biliyan 60b.

Daga cikin korafe-korafe 5,000, ya ce EFCC ta amince da 3,000 domin gudanar da bincike.

Shugaba Bola Tinubu ya nada Olukoyede shugaban EFCC a ranar 12 ga Oktoba, 2023.

Ya maye gurbin Abdurasheed Bawa, wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada.

Daga hawan Tinubu kuma sai ya dakatar da Bawa, aka tsare shi, kuma ya kore shi daga mukaminsa.

More from this stream

Recomended