Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan sun tsere saboda yakin Gaza

Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan ɗaya ne suka fice daga ƙasar kuma ba su koma ba a watanni shida na farkon yaƙin Isra’ila a Gaza.

Wannan na zuwa ne kamar yadda jaridar Times of Israel ta ruwaito, inda ta ambato Hukumar Ƙidaya da Shige da Fice ta ƙasar.

Alƙaluman da hukumomi suka fitar sun nuna cewa Isra’ilawa da suka fice daga ƙasar daga watan Oktoban 2023 sun kai 550,000 — fiye da waɗanda suka koma ƙasar lokacin Easter a watan Afrilu.

Jaridar ta Isra’ila ta ce ƙaurar da ‘yan ƙasar suke yi, wadda da farko ake gani ta guje wa yaƙi ce, yanzu ta zama ta dindindin.

More from this stream

Recomended