Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa.

Atiku ya ziyarci sanata Ningi a gidansa dake babban birnin tarayya Abuja.

A ranar 12 ga watan Maris ne majalisar dattawa ta dakatar na Ningi na tsawon watanni uku bayan da yayi zargin cewa anyi cushe a cikin kasafin kuɗin shekarar 2024.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada goyon bayansa ga tsohon sanatan inda ya ce sanatan ba shi kaɗai ne ba a yaƙin da yake da ya sa aka dakatar da shi.

More from this stream

Recomended