Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane biyu lokacin da suka daƙile yunkurin yin garkuwa da mutane a titin Maraban Jama’a dake Jos a jihar Filato.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi dama faɗin Najeriya baki ɗaya ya ce sojojin sun kuma gano wata mota ƙirar Peugeot.

Bayanai sun ce dakarun a lokacin da suke bincike a yankin sun ceto wani mai suna  Abdul Bello wanda mamallakin motar ne da kuma wata mata mai suna Sekyen Melody Yapshak.

Makama ya ce masu garkuwa da mutane sun sace matar ne daga gidan iyayenta dake kusa da kwalejin ƴansanda ta Jos..

Ya ƙara da cewa an kai mutanen da aka ceto asibitin kwalejin ƴansandan domin a duba lafiyar su a yayin da aka kai motar inda sojojin suke da zama domin cigaba da bincike.

More from this stream

Recomended