Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum ɗaya kuma ya tsira ba tare da ko ƙwarzane ba a wani mummunan hatsarin mota a mahaɗar Gaya dake kan titin Kano-zuwa Maiduguri.

Kwamandan shiyar  Kano na hukumar FRSC dake kiyaye afkuwar  haɗura ta ƙasa, Ibrahim Sallau-Abdullahi shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Abdullahi Labaran ya fitar a ranar Asabar.

Ya ce hatsarin ya rutsa da motoci biyu ɗaya Toyota Hummer mai namba KTG 190 XB  da kuma wata ƙaramar motar a kori kura ƙirar Hijet mai namba KTG 501 YG.

“Mun samu kira da misalin ƙarfe 03:45 na rana a ranar  19 ga watan Afrilu munyi gaggawar tura jami’an mu tare da motar su zuwa wurin domin ceto mutanen da abun ya shafa dai-dai ƙarfe 03:55,”Abdullahi ya ce.

Kwamandan ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da ya kai ga motocin sun yi tawo mu gama suka kuma kama da wuta.

“Hatsarin ya rutsa da mutane 28 dake cikin motocin biyu 11 suka mutu a ciki wasu 16 suka jikkata aka kuma ceto mutum 1 ba tare da ko ƙwarzane bai yi ba,”.

Abdullahi ya ce an yiwa gawar mutanen jana’iza aka bunne su tare a yayin da aka kai waɗanda suka jikkata Asibiti.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...