Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyar APC.

Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock dake Abuja na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan gabanin  fara zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da aka shirya gudanarwa saboda matsin tattalin arziki dake addabar mutane.

Cire tallafin man fetur da kuma dai-daita farashin kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasar waje ta haifar da mummunan tashin farashin kayayyaki.

Akwai rahotannin dake cewa zanga-zangar zata fara ne a makon farko na watan Agusta.

Hope Uzodimma gwamnan jihar Imo da kuma gwamnan jihar Kwara shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Abdurrahaman Abdulrazak su ne suka yiwa gwamonin jagora ya zuwa fadar ta Aso Rock.

Akwai dai kiraye-kiraye daga bangarori da dama dake kiran da ajanye batun zanga-zangar saboda gudun kada ɓatagari su shiga ciki.

More from this stream

Recomended