Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana gaban babbar kotun tarayya dake Abuja.
Hukumar EFCC na son ta gurfanar da Yahaya Bello ne gaban kotu inda take masa tuhume-tuhume 19 da suka shafi almundahana da kuma almubazzaranci da kuɗaɗen da suka kai naira biliyan 82.
Duk da cewa an shirya gurfanar da shi a ranar 18 ga watan Afrilu Bello ya gaza bayyana a gaban kotun.
A yayin cigaba da zaman shari’ar ranar Talata, Adeola Adedipe ɗaya daga cikin lauyoyin Yahaya Bello ya ce wanda yake karewa zai iya bayyana a gaban kotun amma yana tsoron a kama shi a tsare.
“Wanda ake ƙara yana so yazo kotu amma yana tsoron akwai umarnin kotu da ya bada damar a kama shi,” a cewar Adedipe.
Lauyan ya nemi kotun ta soke umarni kamun da aka bayar a ranar 17 ga watan Afrilu.