An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air har sai sai baba ta gani.

Umarnin na zuwa ne biyo bayan hatsarin da ya rutsa da jirgin kamfanin a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos a ranar 23 ga watan Afrilu.

Da safiyar ranar Talata ne jirgin kamfanin da ya taso daga Abuja zuwa Lagos  ya zame daga kan titinsa ya sauka ƙasa dai-dai lokacin da yake sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos.

Hakan ya tilastawa hukumomin filin jirgin karkatar da jiragen masu sauka da tashi ya zuwa ɓangaren da jiragen dake tafiya ƙasashen waje ke sauka da tashi.

A wata wasiƙa mai ɗauke da sahannun  babban sakataren ma’aikatar ta NCAA ,Emmanuel Meribole  ta ce an jawo hankalin ministan kan matukar damuwa da aka nuna kan lamarin.

Ma’aikatar ta ce lamarin ya jawo damuwa kan halin da kamfanin ke ciki ta fuskar kuɗi da kuma matakan kariya.

More from this stream

Recomended