Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar Legas.
Sojojin biyu, Kofur Innocent Joseph da Lance Kofur Jacob Gani, an sallame su ne ba tare da bata lokaci ba tare da mika su ga sauran hukumomin tsaro domin gurfanar da su gaban kuliya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar, ya ce sojojin biyu ne suka aikata laifin a ranar 14 ga watan Afrilu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A bisa kudurin da rundunar sojojin Nijeriya ta yi na tabbatar da kwazo, gaskiya da kuma da’a, hukumar tana son sanar da jama’a sakamakon binciken da aka yi na satar igiyoyin sulke na matatar Dangote a ranar 14 ga Afrilu, 2024, wanda ya haɗa da Kofur Innocent Joseph da Lance Kofur Jacob Gani.
“Bayan wani kwakkwaran bincike da aka gudanar tare da hadin gwiwar jami’an kamfanin, an gano sojojin biyu sun yi watsi da aikinsu da kuma mallakar kayayyakin ba tare da izini ba. Daga nan kuma, an tuhume su da laifin kin yin aikin soja da aka hukunta a karkashin sashe na 57, karamin sashe na (1) da sauran laifukan farar hula da ake hukuntawa a karkashin sashe na 114, karamin sashe (1) na dokar rundunar soji CAP A20, dokar Tarayyar Najeriya ta 2004.
“An musu ƴar ƙwarya-ƙwaryar sharia. A lokacin da ake shari’ar an gabatar da shaidun da ke tuhumar su–su kuma an ba su damar gabatar da kararrakinsu da kuma kare kansu, amma an same su da laifin da ake tuhumarsu da shi kamar yadda dokar soja ta tanada.
“A matsayin nuna rashin amincewar hukumar soji kan rashin da’a da aikata laifuka a cikin jami’anta, an sallami sojojin biyu tare da mika su ga hukumomin da abin ya shafa don ci gaba da gurfanar da su.”