Connect with us

Arewa

SARS: Manyan zanga-zanga biyar da suka rikita gwamnatin Najeriya a shekara 8

Published

on

.

A Najeriya dai, an gudanar da jerin zanga-zanga daban-daban waɗanda suka girgiza gwamnatocin ƙasar, wasu daga ciki kuma har suka kusa kawo cikas musamman ga yanayin gudanar da ƙasar.

Akasarin zanga-zangar da ake yi a ƙasar ana yi ne domin adawa da wani tsari na gwamnati ko kuma nuna rashin goyon baya ga wani mataki da gwamnatin ta ɗauka ko kuma take shirin ɗauka.

Wasu daga cikin zanga-zangar sun yi tasiri wajen kawo sauyi, wasu kuma an yi su ne kawai an tashi ba tare da samun sauyi ko kuma cimma burin wadanda suka fito zanga-zangar ba.

Shafukan sada zumunta a baya-bayan nan sun taimaka matuƙa wurin ƙara rura wutar zanga-zangar da ake yi musamman shafin Twitter, inda ake amfani da mau’du’i domin saurin yaɗa manufa.

Za mu yi dubi dangane da wasu daga cikin zanga-zangar da aka yi da suka girgiza gwamnatoci musamman lokacin mulkin PDP da na APC.

Zangazangar #OccupyNigeria

An fara gudanar da wannan zanga-zangar ne a watan Janairun 2012 a lokacin mulkin mulkin PDP, watanni kaɗan bayan an sake rantsar da Shugaba Goodluck Jonathan a matsayin shugaban ƙasar.

Zanga-zangar ta samo asali ne sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi inda ɗaruruwan mutane suka fito a manyan garuruwa kamar Abuja da Kano da Kaduna har gaban ofishin jakadancin Najeriya da ke Ingila.

A lokacin, wasu masu zanga-zangar sun rufe gidajen mai tare da kulle manyan hanyoyi. Hakazalika manyan ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar sun ayyana shiga yajin aiki har sai an dawo da kuɗin man fetir yadda yake kafin ƙarin da aka yi.

An samu waɗanda suka rasa ransu a lokacin wannan zanga-zangar a jihar Legas da kuma Kwara, da kuma waɗanda suka samu raunuka a wasu jihohin sakamakom arangama tsakaninsu da ‘yan sanda.

Zanga-zangar #BringBackOurGirls

Zanga-zangar BringBackOurGirls ta samo asali bayan da ‘yan ƙunigyar Boko Haram suka sace sama da mata 200 a wata makarantar sakandare da ke Chibok a jihar Borno.

Wannan zanga-zanga ta ja hankalin ƙasashen duniya da shugabanninsu da dama, ciki har da Michelle Obama, matar tsohon shugaban Amurka, sakamakon sace matan masu yawa haka wani abu ne da ba a saba gani ba a duniya.

Mutane da dama musamman mata ‘yan gwagwarmaya sun fito a manyan titunan Najeriya domin neman gwamnatin ƙasar ta karbo waɗannan ‘yan matan.

Akasarin masu zanga-zangar dai kan saka jar riga riƙe da kwalaye ko kuma ƙyallaye ɗauke da saƙonni na buƙatar gwamnati ta ceto ‘yan matan da aka sace.

Gaba-gaba a wannan zanga-zangar, akwai Oby Ezekwesili, Aisha Yesufu, ɗaya daga cikin mai jagorantar zanga-zangar #ENDSARS a Najeriya, da kuma Hajiya Hadiza Bala Usman, shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya a halin yanzu

Duk da alƙawarin da gwamnatin Goodkuck Jonathan ta yi na ceto ‘yan matan, hakan bai sa an daina wannan zanga-zangar ba a ƙasar.

Zanga-zangar #OpenNASS

An gudanar da zanga-zangar OpenNASS domin tabbatar da Majalisar Tarayyar Najeriya na gudanar da ayyukanta a bayyane ba tare da rufa-rufa ba, da kuma rage kuɗin da suke kashewa a matsayin kasafinsu.

Wasu daga cikin buƙatun masu zanga-zangar sun haɗa da buƙatar majalisar ta bayyana ainahin yadda ta ke kashe duka kuɗaɗen da ta kasafta.

Da kuma aikin majalisar ya zama na wucin gadi domin kawo sauƙi ga irin kuɗin da ake kashewa.

Haka kuma masu zanga-zangar sun buƙaci a cire rigar kariya ga ‘yan majalisar ta yadda za a iya gurfanar da su kotu da yanke musu hukunci a ko yaushe.

Zanga-zangar #NotTooYoungToRun

Wannan zanga-zangar dai ta fara ne a shafukan sada zumunta musamman Twitter da mau’du’in #NotTooYoungToRun, wanda kudiri ne na neman bai wa matasa damar takarar mukaman siyasa a kasar.

Hanƙoron da matasan ƙasar suka rinƙa yi ne yasa wannan kudirin har ya kai gaban majalisar tarayyar ƙasar inda a farko aka yi watsi da shi.

Watsi da kudirin ya jawo ɗaruruwan matasan ƙasar bazuwa kan titunan domin gabatar da gangamin kin amincewa da hakan.

Matasan sun fito ne domin neman a ceci kudurin da zai ba su damar tsayawa takarar mukaman siyasa ba sai sun kai wasu shekaru na manyanta ba.

Daga baya dai majalisar asar ta sake zama haka inda ta amince da kudirin har aka tura wa shugaban ƙasar ya kuma saka masa hannu.

Zanga-zangar #ENDSARS

Wannan ita ce zanga-zanga ta baya-bayan nan wadda ta fi jan hankali a ƙasar wadda kuma ta nemi girgiza ƙasar.

Wannan zanga-zangar dai ta fara ne tun tuni a shafin Twitter, inda a duk lokacin da aka samu rikici tsakanin SARS ɗin da wasu ‘yan ƙasar, akan tattauna mau’du’in #ENDSARS a shafin Twitter. Da an tattauna na kwana biyu, sai kuma maganar ta mutu.

Sai dai a baya bayan nan da alama tura ta kai bango, sakamakon zanga-zangar da aka shafe lokaci ana yi a Twitter ta sa mutane suka fara fitowa kan tituna suna gudanar da zanga-zangar.

Garuruwan Abuja da Legas ne kan gaba wurin wannan zanga-zangar inda daga baya jihohi kamar irin su Oyo da Kaduna da dai sauransu suka biyo baya.

Daga cikin manyan fuskokin da ake gani wuri jagorancin wannan zanga-zanga akwai Aisha Yesufu, wata ‘yar gwagwarmaya a Najeriya da kuma Babban Editan Jaridar Sahara Reporters wato Omoyele Sowore.

Duk da matsin lamba da barazana da wasu daga cikin masu zanga-zangar suke samu yayin da suke tattaki, hakan bai sa sun daina ba.

Sai dai bayan an shafe lokaci ana wannan zanga-zangar, gwamnatin ƙasar ta rushe rundunar ta SARS tare da maye gurbinta da SWAT.

(BBC Hausa)

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending