Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam’iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam’iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri daban-daban da ake gudanarwa a Abuja ta neman a sauke shi daga shugabancin jam’iyar.

Amma kuma gwamnatin jihar ta musalta cewa da hannunta a ciki.

Ana dai cigaba da yin zanga-zanga iri-iri dake neman a sauke Ganduje daga shugabancinsa inda kungiyoyin da kuma jagororin jam’iyar daga yankin arewa ta tsakiya suka fi matsa ƙaimi akai.

Ganduje a cikin wata sanarwa ranar Juma’a ta bakin,Kwamared Okpokwu Ogenyi mataimakinsa na musamman kan kungiyoyin farar hula da kuma na magoya baya, ya zargi cewa gwamnatin jihar Kano na hayar mutane waɗansu da yawa ƴan Kwankwasiya da wasunsu suka fito  daga jihohin arewa ta tsakiya inda suke buƙatar Ganduje ya sauka daga muƙaminsa.

Ogenyi ya ce sun samu kwararan bayanai cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na aiki da wasu mutane da suka fito daga shiyar arewa ta tsakiya kuma ya basu maƙudan kuɗaɗe domin su cigaba da zanga-zangar neman a cire Ganduje shugaban jam’iyar ta APC.

Ya yi kira ga jami’an tsaro da suka ido sosai domin kare rayuka da dukiyar jama’a.

More from this stream

Recomended