Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar Kuntau dake ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano.

Ginin ya ruguzo ne lokacin da ake tsaka da aiki da safiyar ranar Juma’a amma kuma ba’asan musabbabin rushewarsa ba.

Aƙalla ma’aikata 11 ake fargabar sun maƙale cikin baraguzai lokacin da lamarin ya faru.

Jami’in tsare-tsare na hukumar ta NEMA a Kano, Nuraddeen Abdullahi ya tabbatarwa da Kamfanin Dillancin Labarai Na Najeriya NAN cewa an samu nasarar ceto mutane biyu a dai-dai lokacin da suka tuntube shi.

Ya ƙara da cewa cikin mutane biyar da aka zaƙulo likitoci a Asibitin Murtala sun tabbatar da mutuwar uku daga ciki a yayin da biyu suka samu raunuka.

More from this stream

Recomended