Connect with us

Arewa

Yawan masu cutar Korona a Najeriya sun zarta 50,000 – AREWA News

Published

on

Yawan mutanen da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ya haura mutane 50,000 a ranar Laraba, bayan da aka samu karin mutane 593 da suka kamu da cutar a jihohi 15 da kuma birnin tarayya Abuja.

A dadin yawan mutanen na ranar Laraba shi ne mafi yawa da aka samu cikin watan Agusta inda jihar Filato ke kan gaba da mutane 186 sai kuma jihar Lagos dake biye mata da mutane 172.

Hukumar NCDC dake dakile yaduwar cututtuka ita bayyana sabon adadin cikin irin sakon da take wallafawa a kowace rana kan halin da ake ciki game da cutar a kasa baki daya.

Kafin ranar Laraba, ranar 5 ga watan Agusta ce ranar da aka samu mutane mafi yawa da suka kamu da cutar cikin watan Agusta.

Hakan na zuwa ne kasa da mako hudu bayan da adadin yawan mutanen ya kai 40,000.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending