Connect with us

Hausa

China ta yi ramuwa kan rufe mata ofishin jakadanci a Amurka

Published

on

The US Consulate-General in Chengdu is pictured on July 23, 2020 in Chengdu, Sichuan Province of China.

Bayanan hoto,
Ofishin jakadancin Amurka na Chengdu

China ta mayar da martani kan rikicin diflomasiyyarta da Amurka wanda ke ƙara ta’azzara.

Mahukuntan Beijing dai sun buƙaci Amurka ta rufe ofishin jakadancinta da ke Chengdu, a kudancin ƙasar.

China dai ta bayyana al’amarin a matsayin halartaccen mataki da ya zama dole.

A wani abu mai kama da idan ka ce kule zan ce ma cas, yanzu dai China ta mayar da martani kan rufe ofishin jakadancinta da Amurka ta ba da umarni a Houston.

China dai ta buƙaci ita ma Amurka ta rufe nata ƙaramin ofishin jakadancin da ke tsakiyar lardin Sichuan na kudancin ƙasar.

Tun a tsakiyar 1980 ne, Amurka ta buɗe ofishin jakadancin na Chengdu.

Daga cikin ayyukansa akwai lura da ayyukan sa-idon gwamnatin Amurka da kuma dangantakarta da yankin Tibet, wanda tsawon lokaci ke fafutuka don ganin hukumomin China sun ba shi ƙarin ‘yanci.

Matakin na zuwa ne bayan Amurka ta umarci China ta rufe ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Houston, inda ta yi iƙirarin cewa matakin yunƙuri ne na kare sirrin Amurkawa da haƙƙin mallakar ƙirƙire-ƙirƙirensu.

China dai ta bayyana matakin a matsayin wani gagarumin keta dokar ƙasashen duniya.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending