Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta CBS ta bada rahoto.

Wani jami’in ma’aikatar wajen Amurka ya faÉ—awa kafar yaÉ—a labaran cewa Kurt Campbell mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka da kuma Ali Lamine Zeine firaministan Æ™asar Nijar sun yi wata ganawa ranar Juma’a a birnin Yamai kan yadda za a shirya ficewar dakarun cikin tsari daga Nijar.

Jami’an biyu sun jaddada muhimmancin dangantaka a tsakanin Æ™asashen biyu inda suka amince su cigaba da haÉ—a kai a fannin da É“ukatar su tazo É—aya.

Ƙasar ta Amurka ta amince ta rufe sansanin sojanta dake garin Agadez inda anan ne ta girke jiragen yaƙinta marasa matuƙi.

Kusan sojan Amurka 1000 ne ke zaune Æ™asar ta Nijar inda suke yaÆ™i da Æ™ungiyoyin Æ´an ta’adda dake yankin Sahel.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...