Connect with us

Hausa

Rikicin Yemen: Me ya sa Burtaniya ke sayar wa Saudiyya makamai?

Published

on

A Yemeni child looks out from behind a wall damaged in an air strike in the southern city of Taez

Bayanan hoto,
Burtaniya ce ke sayar wa Saudiyya makaman da take yaki da su a Yemen

Yayin da aka shiga shekara ta biyar ana tafka yaki a Yemen, alkaluman farar hula da ke mutuwa na karuwa a kullum, sannan Burtaniya ta sake fuskantar matsin lamba kan makaman da take sayar wa Saudiyya.

Ga wasu tambayoyi bakwai masu sarkakiya kan ce-ce-ku-cen.

Me ya hada wadannan kasashen uku wuri guda?

Kasar mai arzikin man fetur ita ce ke sahun gaba wajen sayen makamai a duniya, kuma ita ke jagorantar hare-haren kakkabe ‘yan tawaye a Yemen, wadda ita ce kasar Larabawa mafi talauci a duniya.

A wani rahotan da aka fitar a bara, Burtaniya ta yi ikirarin cewa ita ce kasa ta biyu mafi karfi wajen cinikin makami a duniya, an kiyasta cewa tana sayar da sama da kashi 40 cikin 100 na makamanta ga kasa daya tilo, wato Saudiyya.

Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, da ke kawance da Saudiyya a yakin Yemen, ita ma tana cikin manyan kwastamomi, a cewar wani rahoton gwamnatin Burtaniya da aka fitar a 2019.

Rahotan ya nuna cewa Amurka ce kawai ke gaban Burtaniya wajen cinikin makamai a duniya.

Wane hali ake ciki a Yemen?

Bayanan hoto,
MDD ta yi gargadi kan halin jin-kai na kasashen da ake yaki ke ciki

Majalisar Dinkin Duniya ta binciki a kalla mutuwar farar hula dubu 7,700 a watan Maris din 2020, wanda akasari hare-haren sama da Saudiyya ke jagoranta ke haifarwa.

Sai dai kiyasin sauran kungiyoyin da ke sa ido sun haura wannan alkaluma.

Wata kungiya da ke sa ido kan yaki ta ACLED da ke Amurka, ta ce mutum dubu 100 aka kashe a watan Oktoban 2019, da suka hada da farar hula dubu 12 a hare-haren da aka kai musu kai tsaye.

Kusan kashi 80 cikin 100 na al’ummar Yemen – wato mutum miliyan 24 – ke bukatar agajin jin-kai da kariya.

Yara miliyan biyu aka kiyasta cewa na bukatar abinci mai gina jiki, cikin su dubu 360 ‘yan shekaru kasa da biyar ne.

Me gwamnatin Burtaniya ke cewa?

A lokacin bazara na bara masu fafutikar kare hakkin dan adam sun yi babbar nasara kan gwamnatin Burtaniya, bayan sun hana shigar da makamanta Saudiyya bisa umarni kotu, hakan ya tilasta wa kasar sake nazarin tsare-tsarenta da duba ko hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa a Yemen.

Bayanan hoto,
Burtaniya na taimaka wa Saudiyya da dabarun yaki

Bayan kusan shekara guda, gwamnati ta kammala nazarinta na sanar da cewa za ta dawo da cinikin makamai.

”Saudiyya na da kyakyawar manufa da kuma ikon bin dokar kasa da kasa kan jin-kai,” a cewar sakatariyar kasuwanci ta duniya Liz Truss, hakan ya danne nazarin gwamnati a kan hare-hare.

”Hare-haren da ake nazari a kai sun shafi wadanda ake zargin ko sun karya doka a lokuta da dama, a wuri daban-daban kan dalilai na daban,” a cewar sanarwarta da ta aike wa Majalisar Dinkin Duniya, MDD.

Me masu adawa ke cewa?

Emily Thomberry ta Jam’iyyar Labour, wacce ke magana a madadin ‘yan adawa a hukumar kasuwanci, ta bayyana matakin gwamnati a matsayin ”hujojji marasa karfi”, wadda ta ce sun saba ikirarin gwamnatin Burtaniya na mutunta hakkin dan adam”.

Ta ce gangamin adawa da cinikin makami da aka kai gaban kotu a bara, hukuncin da aka yanke ”babu adalci”.

Bayanan hoto,
Yara miliyan biyu na cikin yunwa sakamakon yaki a Yemen

Kungiyar Airwars da ke da cibiya a Burtaniya na sa ido kan yake-yake da farar hular da ake kashewa a Gabas Ta Tsakiya, ta nuna shakku kan hikimar gwamnatocin da ke taimaka wa Saudiyya.

Kungiyar ta ce akwai shakku kan alkaluman da Burtaniya ke fitarwa na hare-harenta, ballantana a yi batun Saudiyya da suke kawance a yakin.

”Binciken da ya kai wani mataki na rashin sahihanci abin tambaya ne a Burtaniya, kasar da ta amsa cewa ana yi wa farar-hula illa,” a cewar Airways.

Kungiyar ta ba da misali da hare-hare shekaru biyar da Burtaniya ta rinka kai wa a kan kungiyar IS.

A cewar alkaluman gwamnatin Burtaniya, ”Makaman yaki da ISIS 4,400 aka fitar” wanda aka shigarwa Syria da Iraki karkashin dakarun Burtaniya da ke cikin sojojin da Amurka ke jagoranta.

Burtaniya ta ce sojojin Royal Air Force na da alhakin kashe a kalla farar hula guda a yakin.

Airwars, da ta kiyasta kisan farar hula tsakanin dubu takwas zuwa goma, ta ce hanyar da Burtaniya ke bi wajen tattara alkalumanta na mamata ”ba daidai suke ba”.

Nawa ne kudaden da ake magana akansu?

Kungiyar da ke fafutikar adawa da sayar da makamai (CAAT) ta ce Burtaniya ta ba da lasisin makamai na fam biliyan 5.3 ga Saudiyya tun daga shekara ta 2015, lokacin da aka soma yakin Yemen.

A cewar kungiyar, akwai karin biliyoyin fama-famai na kwangilar makamai da ta bayar da lasisinsu ga Saudiyya da kawayenta na yakin Gulf da suke yaki a Yeman tare.

Sai dai CAAT ta ce wadannan alkaluma ba su hada da na makamai da ake sayar da su ba tare da lasisi ba, haka kudaden ribar da ke shigowa.

Kungiyar ta kuma kiyasta cewa cinikin makamin da aka yi a kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen ya kai a kalla ”fam biliyan 16”.

Kayayyakin yakin da aka sayar sun hada da jiragen yaki samfurin Typhoon da Tornado, da kuma bama-bamai.

Jami’an Burtaniya na kuma taimaka wa gamayar kasashen da dabarun yaki da kuma horas da sojojin Saudiyya da ke Burtaniya.

Burtaniya kawai ke sayar da makamai?

Yawan makaman da Burtaniya ke sayarwa bai taka kara ya karya ba duk da cewa tana cinikin nata a yankunan Atlantic har zuwa Saudiyya.

Kashi kusan 70 cikin 100 na makaman da Saudiyya ta saya tsakanin 2015 zuwa 2019 na zuwa ne daga Amurka, a cewar rahotan cibiyar bincike ta Stockholm (SIPRI).

Kasa ta biyu a jadawalin bincike ita ce Burtaniya, wacce ke sayar da kashi 13 cikin 100 na yawan makamin, sannan Faransa da ke ta uku da kaso 4.3 cikin 100.

Bayanan hoto,
Mayakan Houthi sun yi watsi da tsagaita wuta

Kusan rabin makamin da Amurka ke sayarwa a cikin shekarun biyar da suka gabata na zuwa ne Gabas Ta Tsakiya, kuma rabin wannan adadin Saudiyya ake tura su, a cewar Pieter D. Wezeman, babban jami’in bincike a SIPRI.

Shugaba Trump na Amurka ya bayyana kasar Saudiyya da kawarta UAE a matsayin ”gungun kasashen da ke aikata ta’asa a Gabas Ta Tsakiya”.

Akwai kyakkyawan zato cewa ‘yan tawayen Houthi da kawancen Saudiyya ke yaka a Yemen na samun goyon bayan Iran, zargin da Tehran ta sha musantawa.

Wane irin hasashen ake kan makoma?

Sakataren harkokin wajen Burtaniya, Dominic Raab a wata makala da ya wallafa a jaridar Financial Times, ya bayyana cewa gwamnatin Burtaniya na kokarin kawo zaman lafiya a Yemen da kuma ba da gudunmawa a fannin jin-kai.

Gwamnati ta sha kiran tsagaita wuta a Yemen, ya kara da cewa Burtaniya da Jamus da Sweden na neman taimakon hadin-gwiwar dala miliyan 365 a wannan shekarar domin taimaka wa ayyukan MDD a kasar.

Baya ga barkewar cutar kwalara da aka samu, Yemen na kuma fama da annobar Covid-19, ga shi kuma rabin asibitocin kasar kawai ke aiki.

Bayanan hoto,
The UN fears coronavirus deaths could dwarf the loss of life during the war MDD na fargabar cewa mace-mace sakamakon cutar korona ka iya rage mace-mace sakama

A watan Afrilu, Saudiyya ta sanar da tsagaita wuta a kasar saboda annobar korona.

Sai dai mayakan Houthi sun yi watsi da tsagaita wutar, inda suka bukaci a cire haramcin da aka sa a fanin sufurin jiragen sama dana ruwa a birnin kasar, Sanaa da tashar ruwan Hudaydah.

A yanzu, haramcin na ci gaba da aiki, MDD kuma ta gargadi cewa yakin a nan gaba na iya zarta abin da aka gani a baya.

Kungiyar ta ce alkaluman mamata sakamakon annobar korona na iya ”zarce alkaluman mamata sakamakon yakin kasar da cutuka da yunwa na cikin shekaru biyar”.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending