Connect with us

Arewa

‘Yan Boko Haram ‘sun kashe sojojin Jamhuriyar Nijar 12 a Diffa’

Published

on

Getty

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tun 2015 Jihar Diffa ke fuskantar hare-hare daga ‘ya’yan ƙungiyar Boko Haram

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutuwar dakarunta 12 yayin da 10 kuma suka jikkata lokacin wani hari da aka kai musu a garin Blabrin na jihar Diffa.

Hakan na cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar aka karanta ta a gidan talabijin na kasar Télé Sahel.

Gwamnatin ta cikin sanarwar ta ce “a gabashin garin Guiguimi na jihar Diffa sansanin sojin kasar mu ya fuskanci hari daga kungiyar Boko Haram dauke da muggan makamai”.

Sanarwar ta kara da ce maharan sun cinna wa kayan yaƙi da dama wuta suka kuma yi awon gaba da wasu masu tarin yawa.

Cikin gaggawa rundunar sojin Guiguimi suka bi sahun maharan wanda haka ya basu damar kashe 7 cikinsu tare da kwato daukacin makaman da suka kwashe daga ciki hadda motar igwa.

Sanarwar ta kara da cewa kuma daukacin sojin da aka ambato sun ɓata sun koma bakin daga. Har yanzu kuma dakarun sojin na cikin daji suna don neman sauran maharan dan ƙarasa kakkaɓe su.

Wannan yanki na Guiguimi da ke da iyaka da ƙasar Chadi, na fama da hare-haren mayakan Boko Haram bangaren Abu Musab Albarnawi da ya yi mubayi’a ga ƙungiyar IS tun shekarar 2016.

Tun 2015 Jihar Diffa ke fuskantar hare-hare daga ‘ya’yan ƙungiyar Boko Haram, daga baya hare-haren sun ɗan lafa a kashen 2019, kafin ranar 7 ga watan Maris din bana, da suka ƙaddamar da wani hari a garin Shetimari inda suka kashe dakaru 8 har lahira.

Trending