Connect with us

Arewa

‘Mun kama jirgin Burtaniya mai fasakaurin jama’a zuwa Najeriya’

Published

on

Hadi Sirika

Hakkin mallakar hoto
Twitter

Image caption

Ministan sufurin jirage, hadi Sirika ya ce za su hukunta kamfanin jirgin idan sun same shi da laifi

Gwamnatin Najeriya ta ce ta kama wani jirgin sama mallakar wani kamfani da ke Burtaniya bisa zarginsa da yin jigilar Fasinjoji zuwa cikin kasar duk da hanin da aka saka na yin hakan saboda annobar korona.

Ministan sufurin jiragen sama na kasar Hadi Sirika wanda ya sanar da hakan, ya ce an ba jirgin na kamfanin Flair Aviation ne iznin jigila zuwa cikin kasar don taimaka wa wajen ayyukan jinkai, amma kuma ya fake da hakan wajen soma jigila irin ta kasuwanci.

Hadi Sirika ya kara da cewa abin ya ba su mamaki inda suka tsare jirgin sannan ana gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ke faruwa.

Ministan dai ya yi zargin abin da ya kira “suna bincike domin gano ko akwai wani abu da ake rufe musu kuma idan muka same kamfanin da laifi za mu hukunta shi daidai gwargwado.”

  • Coronavirus: Shin maganin Madagascar tazargade ne?
  • Coronavirus: Yadda wata mata suke taimaka wa marasa galihu

Ya ce gwamnatin Najeriya ta yi shigar burtu inda ta gano yawan kudin da ake biyan jirgin domin kai jama’a Najeriya.

Sai dai kuma ministan bai fadi tsawon lokacin da jirgin ya kwashe yana gudanar da ‘haramtattun ayyukan’ da gwamantin Najeriyar ke zargin kamfanin.

Har kawo yanzu dai kamfanin Flair Aviation bai ce uffan ba dangane da zargin kuma da zarar ya mayar da martani za mu sanar da jama’a.

Trending