Connect with us

Hausa

‘Kashi 34 cikin 100 na ‘yan Najeriya ke amfani da kwaroron roba’ – Rahoto

Published

on

Condom

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani sabon bincike ya nuna cewa kashi 34 cikin 100 ne kacal na ‘yan Najeriya suke amfani da kwaroron roba yayin jima’i, kuma cikin wannan yawan kashi 28 cikin 100 ne kawai ke amfani da shi ko yaushe.

Kungiyoyin da suka hada kai wajen yin binciken sun hada da cibiyar NOI Polls mai yin bincike kan wasu al’amura a Afirka Ta Yamma da Hukumar Takaita Yaduwar Cutar AIDS NACA da kuma Gidauniyar AIDS HealthCare Foundation (AHF).

Shugaban NOI polls Dr Chike Nwangwu, Dr Chike Nwangwu, ya shaida wa BBC cewa duk da cewa kashi 83 cikin 100 na ‘yan Najeriya sun yi amannar cewa mutanen kirki ne kawai ke amfani da kwaroron roba, kuma kashi 34 ne kawai suka yarda suke amfani da shi.

“Kuma ko cikin kashi 34 din ma kashi 28 ne kawai ke amfani da shi ko yaushe.”

An fitar da rahoton ne don bikin Ranar Kwaroron Roba ta Duniya (ICD), da ake yi duk 13 ga watan Fabrairu, kwana guda kafin ranar Valentine, don wayar da kai kan masu son yin jima’i da kariya, ake kuma karfafa wa mutane su yi amfani da kwaroron roba.

  • An yi kiranyen kwaroron roba a Uganda
  • An yi sabon kwaroron roba don sojoji

Oga Nwangwu, ya ce ‘yan Najeriya ba sa shan wata wahala wajen sayen kororon robar, saboda kaso 82 cikin 100 na samun sauki wajen siya.

Ya ce a bangaren Kudu maso Gabashin Najeriya, kaso 94 cikin 100 na mazan yankin sun ce sayen kororon roba a wajensu, kamar sayen biskit ne.

Yawancin ‘yan Najeriya dai, sun ce ya kamata a ce ana bayar da kororon roba kyauta, amma wasu sun ce kamata ya yi a rinka sayar da shi a kan naira 100.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Dalilan da ya sa wasu ba sa amfani da kororon roba

  • Wasu kan ce amfani da kororon roba ya sabawa addininsu
  • Wasu kuma kan ce dalilinsu shi ne saboda matansu ba sa so
  • Wasu kuwa kan ce ai matansu daya don haka ba sai sun yi amfani da kororon roba ba
  • Wasu cewa suke ba su da sha’awar amfani da shi ma
  • Wasu kuwa kan ce amfani da shi babu dadi.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending