Connect with us

Arewa

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 100 tare da kwato makamai a Zamfara da Katsina – AREWA News

Published

on

Rundunar sojojin Nijeriya sashin ‘Operation Hadarin Daji,’ sun yi nasarar kashe ‘yan bindigar da suka ki mikawa wuya 100 tare da manyan kwamandojin ‘yan bindigar 6 a jihohin Katsina da Zamfara.

Jami’in watsa labarai na rundunar sojojin Kaftin Ayobami Oni-Orisan, ne ya sanar da hakan.

Ayobami, ya ce rashin mikawa wuya ga gwamnatin jihar Zamfara da ta bullo da shi yasa dakarun suka yi farautar ‘yan bindigar, hakan yasa suka yi nasara kashe su.

Ya kara da cewa, daga ranar 16 ga Disamba 2019 zuwa 9 ga Janairu 2020, dakarun sojojin Najeriya tare da takwarorin su na sama da na ruwa da rundunar ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaron farin kaya DSS da sauran jami’an tsaro sun gudanar da farmaki ga ‘yan bindigar don tabbatar da zaman lafiya a yankunan jihohin.

Trending