Connect with us

Hausa

An kashe ‘yan Amurka 9 a harin Mexico

Published

on

Photo of Rhonita Miller and her family

Hakkin mallakar hoto
CBS news

Akalla Amurkawa tara ne suka mutu ciki har da yara shida a wani hari da wasu da ake zargin gungun masu safarar kwayoyi ne suka kai kan wani ayarin motoci a arewacin Mexico.

Wadanda aka kashe na daya daga cikin iyalan gidan LeBaron, wadanda sun dade zaune a Mexico inda suka hada mata uku da yara guda shida.

Ministan tsaron Mexico ya bayyana cewa mai yiwuwa ne wadanda suka kai harin ba wadannan ayarin motocin suka yi niyyar kai wa harin ba, kila akwai wasu na daban da suke dakon su, sai suka far wa ayarin.

Jihar Sinora da ke arewacin Mexico dai na da gungun masu safarar kwayoyi biyu masu rikici da junansu da suka hada da La Línea, wadda take da alaka da gungun Juárez.

Sai kuma abokiyar adawar ta wato Los Chapos wadda tana cikin gungun Sinaloa.

Iyalen wadanda lamarin ya shafa sun tattauna da jaridar New York Times kuma sun shaida cewa cikin yaran biyu da aka kashe basu kai shekra daya da haihuwa ba.

A wani sakon Twitter na Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana wadanda aka kashe a matsayin abokan arziki wadanda fada tsakanin gungun masu safarar kwayoyi ya rutsa da su.

A cikin jerin sakonnin ya bayyana cewa Amurka a shirye take da ta kai dauki ga kasar.

Shugaban Mexico Andrés Manuel López Obrador, ya bayyana cewa Mexico za ta dauki mataki da kuma kokarin kamo wadanda suka kai harin.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending