Connect with us

Hausa

Tsigewa daga mulki: ‘Yan Republican sun fara juya wa Trump baya

Published

on

Donald Trump boards Air Force One to travel to Texas, 12 January

Wani yunkuri da ‘yan jam’iyyar Democrat ke yi na tsige Shugaba Donalad Trump na Amurka na kara samun goyon baya daga ‘yan jam’iyyar shugaban.

Dan majalisa na uku mafi mukami a majalisar wakilai, Liz Cheney ta ce za ta kada kuri’ar tsige Mista Trump kan zanga-zangar da aka yi wadda ta shafi majalisar kasar a amakon jiya.

Tun da farko shugaban ya ki daukan alhakin abin da ya auku.

Ranar 20 ga watan nan Joe Biden zai gaje shi.

Majalisar wakan ta shirya kada kuri’a kan tuhumar da ta ke ma sa na zuga mabiyansa da su yi yunkurin tumbuke gwamnati, matakin da zai ba Mista Trump lambara yabo ta shugaban da aka tsige har sau biyu a tarihin Amurka.

Wai me ‘yan Republican su ka ce ne?

Ms Cheney, wadda ‘yar tsohon mataimakin shugaban kasa Dick Cheney ce, ta lashi takobin mara wa yunkurin tsige shugaban baya, a karon farko da wani shugaba cikin jerin shugabannin jam’iyyar shugaban kasa ya dauaki irin wannan matakin tun zamanin tsohon shugaba Richard Nixon.

Ga abin da ta ce cikin wata sanarwa: “Ba a taba samun irin wannan aikin cin amana daga shugaban Amurka ba kan ofishinsa da rantsuwar da ya dauka ta kare tsarin mulki.”

‘yar majalisar da ke wakiltar wata mazaba a jihar Wyoming ta kara da cewa “Mista Trump ya aika da gungun ‘yan dabarsa, kuma shi ne ya cinna wutar harin da su ka kai.”

Akwai kuma wasu ‘yan jam’iyyar Republican biyu da su ka mara wa wannan yunkurin baya: John Katko da Adam Kinzinger.

A karon farko bayan da gungun mabiyansa su ka kai hari cikin majalisar Amurka, Mista Trump ya bayyana a idon jama’a, kuma bai nuna nadama ba yayin da ya ke yin jawabi ga magoya bayansa a kusa da kan iyakar Amurka da Mexico a jihar Texas.

Ya ce: “Kalaman da na yi amfani da su sun yi daidai da lokacin da na fade su.”

Ya kuma sanar da manema labarai cewa: “Wannan yunkurin tsige ni yana tayar da hankulan mutane, kuma kuna ci gaba da yin haka, lallai ba abu ne mai kyau da su ke yi ba.”

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending