Connect with us

Arewa

Abubakar Shekau: Iswap ta tabbatar da mutuwar shugaban Boko Haram

Published

on

Abubakar Shekau

Asalin hoton, AFP

Shugaban ƙungiyar Boko Haram a Najeriya, Abubakar Shekau, ya kashe kansa, kamar yadda wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ke hamayya da Boko Haram ɗin ta bayyana a sautin wata murya da aka naɗa.

A cikin sautin, wanda kamfanonin dillancin labarai suka samu, ƙungiyar Iswap ta ce Shekau ya mutu ne a lokacin da ya kunna abin fashewa a jikinsa bayan karawa tsakanin ƙungiyoyin biyu.

Dama dai a watan da ya gabata ne rahotannin mutuwar tasa suka bayyana sai da ba wannan ne karon farko ba.

Kawo yanzu, ƙungiyar ta Boko Haram da gwmnatin Najeriya ba su tabbatar da mutuwar tasa ba.

Me sautin muryar da aka naɗa ke cewa?

A sautin wanda ba a san lokacin da aka naɗe shi ba, wata murya da ake tunanin ta shugaban Iswap Abu Musab al-Barnawi ce, ta ce “ya kashe kansa nan take ta hanyar kunna abin fashewa”.

Mayakan Iswap sun gano shugaban ƙungiyar Boko Haram ɗin ne kuma suka ba shi damar tuba ya koma cikinsu, a cewar al-Barnawi.

“Shekau ya gwammaci ya tozarta a lahira da ya tozarta a duniya,” a cewarsa.

Lokacin da rahotannin mutuwar Shekau suka bayyana a cikin watan da ya gabata, rundunar sojin Najeriya ta ce za ta bincika.

Mai magana da yawun rundunar, Burgediya Janar Mohammed Yerima a lokacin ya shaida wa BBC cewa rundunar na bincike kan abin da ya faru, amma ba za ta fitar da sanarwa ba sai ta samu tabbacin mutuwar tasa.

Wani ɗan jarida da ke da alaƙa ta kut da kut da jami’an tsaro ya ce Shekau ya mutu a lokacin da Iswap suka kai wa Boko Haram hari a dajin Sambisa, a arewa maso gabashin Najeriya.

Dama ko a baya an sha cewa ya mutu, amma sai ya sake bayyana.

Wane ne Abubakar Shekau?

Bayan ƙwace ragamar Boko Haram bayan mutuwar wanda ya kafa ta a hannun ƴan sanda a shekarar 2009, Shekau ya jagoranci sauya ƙungiyar daga wata ƙungiya ta bayan fage zuwa mai kai munanan hare-hare da ta mamaye arewa maso gabashin Najeriya.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shekau ya yi amfani da bidyon farfaganda don tallata aƙidarsa mai muni

Ƙarƙashin jagorancin Shekau, Boko Haram ta shirya hare-haren ƴan bindiga da garkuwa da mutane da fasa gidajen yari a faɗin yankin. Kuma daga shekarar 2014, ta fara mamaye birane da niyyar kafa Ƙasar Musulunci ƙarƙashin dokokin Shari’a.

Shekau, wanda ake tunanin yana cikin shkearunsa na 40, ya goyi bayan wani mummunan kamfe na iƙirarin jihadi a hotunan bidiyo masu cike da farfaganda da ke da kamanceceniya da na Osama Bin Laden.

“Ina jin daɗin yin kisa…yadda na ke jin daɗin yanka kaji da raguna,” ya ce a wani bidyo da ya fitar a 2012.

Tun da ya zama jagoran kungiyar, an kashe sama da mutum 30,000 tare da raba sama da mutum miliyan biyu daga muhallansu.

Ƙungiyar ta ja hankalin duniya bayan da ta yi garkuwa da ɗaruruwan ɗalibai ƴan mata daga wata makaranta a Chibok, a jihar Borno a shekarar 2014 wanda ya haifar da kamfe din #BringBackOurGirls. Har yanzu ba a gano wasu daga cikin ƴan matan ba.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending