Connect with us

Hausa

Nemanja Matic zai ci gaba da zama a Manchester United zuwa 2023

Published

on

Matic and De Gea

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Matic ya koma Manchester United daga Chelsea a shekarar 2017

Dan kwallon Manchester United, Nemanja Matic ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar zuwa karshen kakar 2023.

Dan wasan tawagar Serbia, mai shekara 31 ya koma United daga Chelsea a 2017 wanda yarjejeniyarsa zai kare a Old Trafford a karshen Yunin 2021.

Ole Gunnar Solskjaer ya ce ”Ya yi murna da Matic zai ci gaba da taka leda a United, na san kwarewarsa da iya jagorancinsa zai taimaka wajen bunkasa matasan ‘yan kwallon da muke da su.”

“Nemanja yana kaka ta uku a Old Trafford kawo yanzu, ya kuma san mahimmacin buga wa Manchester United kwallo da kare martabarta.”

Matic ya yi wa United wasa 27 a dukkan fafatawa a kakar bana.

Kungiyar ta Solskjaer ba ta yi rashin nasara a wasa ba tun daga watan Janairu – karawa 16 kenan a jere a dukkan fafatawar da ta buga – tana ta biyar a kan teburin Premier League na bana..

Haka kuma United ta kai wasan daf da karshe a FA Cup a bana tana kuma cikin gasar zakarun Turai ta Europa League.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending