Connect with us

Hausa

Mariappa dan wasan Watford na dauke da korona

Published

on

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Dan kwallon Watford Adrian Mariappa ya ce yana daga cikin mutum uku da ke dauke da cutar korona a kulob din.

A ranar Talata ne aka sanar da cewa mutum shida a kungiyoyi uku na gasar Firemiya na dauke da korona.

Ma’aikata biyu a Watford da kuma mataimakin manajan Burnley, Ian Woan ma duk suna dauke da cutar.

“Abin mamaki ne saboda ban cika fita daga gida ba,” in ji Mariappa mai shekaru 33.

“Ban da atisaye yawanci a gida nake komai”.

Dan kwallon na Jamaica ya ce bai ji wata alamar cutar ba.

Trending