Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin a É—aura musu aure.

Gwamnan ya rattaba hannu ne akan dokar a wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar a gidan gwamnati jihar da ya samu halartar shugaban majalisar dokokin jihar.

A cewar mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa daga yanzu babu wani aure da za a É—aura a jihar ba tare da an gabatar da takardar shedar yin gwaje-gwajen ba

Gwaje-gwajen sun haÉ—a da na ciwon hanta, cutar HIV, Æ™wayoyin halitta da kuma sauran cututtukan da za iya É—auka ta hanyar jima’i.

Ya ce dokar ta zama dole domin kawo ƙarshen yaran da ake haifa da cutar sikila, HIV da kuma cutar hanta.

More News

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...

Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus...

Kotu ta yanke wa É—ansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin...