
Kwamishinan shari’a na jihar Ondo ya tabbatar da shirin da ake yi na binciken musabbabin mutuwar, Rotimi Akeredolu tsohon gwamnan jihar.
Akeredolu wanda babban lauya ne mai mukamin SAN ya taba rike mukamin shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya NBA ya mutu a ranar 27 ga watan Disamba 2023.
A ranar Litinin kwamishinan shari’a na jihar Ondo Olukayode Ajulo ya ce ma’aikatar shari’a ta jihar ta karbi korafe-korafe daga mutane da dama dake kira a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar Akeredolu.
Ajulo ya ce a karkashin dokar gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar mutum ta jihar Ondo al’umma na da hakkin bukatar karin haske kan mutuwar mutum musamman idan aka yi zargin akwai sakaci ko kuma akwai abubuwan da suka shige musu duhu dake bukatar karin haske.
Ya ce korafe-korafen sun fito ne daga kungiyoyin kwararru da kuma mazauna garin Owo mahaifar tsohon gwamnan.