An daure fasto shekaru 25 kan laifin yi wa yarsa mai shekaru 14 fyade

Wata kotun hukunta laifuka na musamman dake Ikeja a jihar Lagos ta yankewa wani fasto mai suna Ndukwe Ogbu mai shekaru 45 daurin shekaru 25 a gidan yari.

Kotun ta samu Ogbu da aikata laifin yi wa yarsa mai shekaru 14 fyade.

A ranar Litinin mai shari’a Olubunmi Abike-Fadike dake sauraren karar ta yankewa wanda ake kara hukunci kan tuhume-tuhume uku da ake masa da suka hada da cin zarafi, aikata lalata da kuma cin zarafi ta hanyar jima’i.

Da ta ke yanke hukuncin mai shari’a, Abike-Fadike ta ce masu gabatar da kara sun gamsar da kotu da kwararan hujjoji dake tabbatar da cewa wanda ake kara ya aikata laifin.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya na NAN mai shari’ar ta ce Ogbu bai nuna wata nadama ba na laifin da ya aikata lokacin da yake rokar kotun ta tausaya masa saboda yana da wasu yayan.

More from this stream

Recomended