Yan bindiga sun kashe DPO a Sokoto

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe DPO na caji ofis din yan sanda dake kauyen Gidan Madi a karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.

Har ila yau sun kashe karin wani dan sandan kafin su yi awon gaba da wasu matan wani fitaccen dan kasuwa a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ne da misalin karfe daya na dare.

Yan bindigar sun kashe yan sandan ne a harin kwanton bauna da suka yi musu lokacin da suka yi kokarin kwato matan.

More News

Peter Obi Ya Ziyarci Mutanen Da Su Ka Ƙone Sakamakon Wutar Da Wani Ya Cinnawa   Masallaci A Kano

Ɗan takarar shugaban ƙasa  a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam'iyar Labour Party (LP) Peter Obi ya ziyarci mutanen da wani matashi ya cinnawa wuta a...

An sanar da zaman makoki na kwana biyar saboda mutuwar shugaban kasa a Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi...

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...