El-Rufai zai kwana a ofishin EFCC

Hukumar EFCC dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai kamar yadda wasu majiyoyi dake hukumar su ka tabbatar.

El-Rufai wanda jigo ne a jam’iyar adawa ta ADC ya mika kansa bisa ga EFCC a ranar Litinin biyo bayan gayyatar da ta yi masa domin ya amsa wasu tambayoyi.

A cewar majiyar dake hukumar tsohon gwamnan zai kwana a tsare a ofishin saboda rashin kammala tambayoyi da jami’an hukumar su ke yi masa.

” E yana tsare a hannun mu kuma zai kwana ne anan,” a cewar majiyar.

Majiyar ta kara da cewa za a iya sakin tsohon gwamnan a ranar Talata bayan an kara sa yi masa tambayoyi.

Tun da farko dai sai da jami’an yan sanda su ka yi artabua harabar hukumar da wasu masu zanga-zangar goyon bayan tsohon gwamnan.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]