EFCC ta kama matasan da suka share majina da ₦500

Hukumar EFCC dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta kama wasu matasa uku da aka zargi da cin zarafin takardar kuɗin naira.

Jami’an hukumar da suka fito daga ofishin hukumar na shiyar Maiduguri ne suka kama matasan a birnin Maiduguri.

Matasan da aka kama sun haɗa da Adam Muhammad, Muhammad Muhammad da kuma Bashir Musa.

An kama Adam, Bashir da kuma Musa ne bayan a wani fefen bidiyonsu ya karade soshiyal midiya inda aka gansu suna share majina da takardar kuɗin naira ₦500.

Bayan sakin bidiyon ne jami’an hukumar suka gano mutanen uku suka kuma kama su a birnin Maiduguri.

Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]