Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya jagoranci rabon tallafin abinci da gwamnatin tarayya ta bayar ga iyalai sama da 10,000 a karamar hukumar Mafa.
An gudanar da rabon kayayyakin ne a ranar Talata a cibiyoyi hudu da ke garin Mafa, hedikwatar karamar hukumar.
Kowanne daga cikin masu gidaje 10,000 ɗin ya samu tallafin da ya kunshi buhun masara mai nauyin kilogiram 50.
Zulum ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin tarayya bisa wannan shiga tsakani da aka yi, ya kuma bayyana cewa an raba wasu kayan abinci a Gwoza da Nganzai.