Sojoji sun yi luguden wuta wa ƴan ta’adda a Kaduna

Rundunar sojin sama ta Najeriya NAF ta ce ta kashe ‘yan ta’adda da dama a Tsauni Doka da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce rundunar ta NAF na Operation Whirl Punch ce ta kai harin.

Mista Gabkwet ya ce an kai harin ne bayan wasu sahihin bayanan sirri sun nuna akwai wani shugaban ‘yan ta’adda da aka fi sani da Boderi da sojojinsa a Tsauni Doka.

Ya ce an kai hare-haren ta sama a wurin da sanyin safiyar ranar 16 ga watan Nuwamba, wanda ya haifar da mummunan sakamako ga ‘yan ta’addar.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]