Rundunar Sojan Saman Najeriya Ta Kashe Abu Asad Jigo A Ƙungiyar Boko Haram

Bangaren sojan sama na rundunar Operation Hadin Kai ya sanar da kisan Abu Asad ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Boko Haram.

Ƙarin Æ´an ta’ada da dama aka bada rahoton sun mutu a harin da jiragen yaki suka kai musu a maboyar su dake Tagoshe a tsaunukan Mandara.

Edward Gabkwet daraktan yaÉ—a labarai na Rundunar Sojan Saman Najeriya shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Asabar a Abuja.

Gabkwet ya ce an kai farmakin ne a ranar Juma’a inda ya ce harin na daga cikin mafi nasara da bangaren sojan sama na rundunar Operation Hadin Kai ya kai a ƴan kwanakin nan.

Ya ce kafin kai harin sojojin saman sun ga Æ´an ta’adda kusan sama da É—ari tare da wasu motocin yaÆ™i huÉ—u suna ta tattaunawa suna raha a tsakanin su a wurin dake da wasu gine-gine uku.

“Biyo bayan kai harin biyu daga cikin ginin sun rushe tare da dukkanin motocin yaÆ™in da aka lalata su”

“Akwai alamu dake nuna cewa Abu Asad wanda Æ™usa ne a Boko Haram bangaren Ali Ngulde da kuma sauran yan ta’ada kamar su Ibrahim Nakeeb, Mujaheed Dimtu, Mustafa Munzir da sauransu na daga cikin Æ´an ta’adda da dama da aka kashe a harin.” a cewar sanarwar.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...