Sojoji sun  kashe mayaƙan ISWAP 15 a wani hari ta sama

Aƙalla mutane 15 ne da ake zarginsu da kasancewa mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne aka kashe a wani harin jirgin sama marar matuki a karamar hukumar Marte ta jihar Borno.

A cewar kafar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi dama Najeriya baki ɗaya an kai harin ne a ranar Talata da ƙarfe 05:35 na asuba bayan da bayanan sirri suka nuna mana cewa akwai ƴan ta’addan a wajejen yankin KLA Balia dake ƙaramar hukumar Marte.

Kafar yaɗa labaran ta bayyana cewa jirgin saman marar matuki dake tattara bayanan sirri wanda aka yi wa laƙabi da ” Guardian” shi ne ya gano wasu motoci uku da aka ɓoye su a wurare daban daban kafin daga bisani jirgin ya gano wasu mutane biyar da suka ɓuya a kasan bishiya.

Makama sun kara da cewa bayan jirgin ya tabbatar da mutanen sai ya harba musu bam inda ya kashe su nan take a yayin da fashewar wasu abubuwa a wurin ta yi asarar rayukan sauran mutanen hakan ya sa yawan waɗanda suka mutu ya ƙaru ya zuwa mutane 15.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]