Mutuwar Attahiru Za Ta Mayar Da Hannun Agogo Baya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kwatanta rasuwar babban hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a matsayin wani abu da zai haifar da koma baya ga kasar.

Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a sa’o’i bayan rasuwarsa.

Janar Attahiru ya rasu ne a wani hadarin jirgi da ya auku a kusa da filin tashin jirage da ke Kaduna a arewa maso yammacin kasar.

“Hadarin jirgin, ya yi mana kwaf daya a makasa, a kuma daidai lokacin da dakarunmu suka samo bakin zaren kawo karshen matsalar rashin tsaro da kasar ke fuskanta.” Buhari ya ce a sanarwa ta Shehu wacce ya wallafa a shafin Twitter.

Buhari wanda ya yi addu’a ga mamatan, ya sha alwashin ba za a manta da irin saudakarwar da suka yi ba.

A watan Janairu, Buhari ya nada Janar Attahiru, wanda ya gaji Janar Tukur Buratai tare da sauran hafsoshin sojojin kasar.

Wannan shi ne karo na uku a wannan shekara da jirgin sojin Najeriya ke yin hatsari ko ya bata a neme shi a rasa.

Lokacin da ministan tsaron Najeriya yake yi wa Shugaba Buhari kan hadarin jirgin (Twitter/@BashirAhmaad)
Lokacin da ministan tsaron Najeriya yake yi wa Shugaba Buhari kan hadarin jirgin (Twitter/@BashirAhmaad)

A halin da ake ciki fadar shugaban kasar, ta fitar da sunayen mutum 11 da suka mutu a hatsarin jirgin:

– Lt Gen. I. Attahiru

– Brig Gen. MI Abdulkadir

– Brig Gen. Olayinka

– Maj. LA Hayat

– Maj. Hamza

– SGT Umar

Matuka Jirgin Da Masu Hidima

– FLT LT TO Asaniyi

– FLT LT AA Olufade

– ACM Oyedepo

More News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...