Gbajabiamila zai yi murabus daga majalisar wakilai a yau

A yau ne ake sa ran Femi Gbajabiamila, tsohon kakakin majalisar wakilai zai yi murabus daga majalisar wakilai.

Domin karbar ragamar shugabancin ma’aikatan fadar shugaban kasa karkashin Bola Tinubu.

Ku tuna cewa an nada Gbajabiamila a matsayin babban hafsan ma’aikatan shugaba Tinubu a ranar 2 ga watan Yuni.

Bugu da kari, shugaban ya nada Sen. Ibrahim Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata da George Akume, tsohon ministan ayyuka na musamman a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]