Hukumar NDE dake samar da aikin yi a Najeriya ofishin jihar Sokoto ya fara yin rijistar mara sa aikin yi a jihar da suka fito daga kananan hukumomin jihar 23.
Shugaban sashen tsare-tsare,bincike da kuma kididdiga na hedkwatar hukumar dake Abuja, Mallam Umar Aliyu shi ne ke sanya ido kan shirin tare da Sulaiman Adamu Kangiwa wakilin shugaban shirin a jihar.
Ana gudanar da aikin yin rijistar ne a ofishin hukumar ta NDE dake jihar da kuma a kananan hukumomi 23 na jihar.
Da suke zagawa domin ganin yadda shirin ke gudana jami’an su bayyana gamsuwar su kan yadda shirin ke gudana ba tare da wasu matsaloli ba.
An dai fara shirin ne a ranar 17 ga watan Afrilu inda za kuma a kammala ranar 9 ga watan Mayu.
