Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Karamar Hukuma Bayan Kashe Dogarinsa A Taraba

Wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace, Boyi Manja shugaban karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a garin Kofai-Ahmadu dake kan hanyar Takum-wukari a jihar.

Yan bindigar sun kuma kashe dogarinsa lokacin da suke ƙoƙarin yin garkuwar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda ya ce yan sandan na cigaba da bincike dazukan dake yankin domin ceto Manja.

More News

Ɗalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...