Wani mutum ya halaka bayan ya zunduma cikin rijiya

Wani ɗan shekara 25 Banji Adebayo a Jihar Kwara ya faɗa rijiya, wanda hakan ya yi sanadiyar rasa rayuwarsa.

Al’amarin dai ya faru ne a Ile-Nla da ke Omu-Aran a ƙaramar hukumar Irepodun.

Rahotanni sun nuna cewa lokacin da Banji yake ɗiban ruwa a rijiyar ne ƙafarsa ta subuce kawai sai ya tsunduma cikinta.

Jami’an kwana-kwana tuni suka kawo ɗauki suka ciro gawar a misalin ƙarfe 5 zuwa shida na Asabar yau Litinin.

More News

Ƴan ta’adda sama da 260 sun miƙa wuya ga jami’an tsaro

Yayin da dakarun Operation Lake Sanity 2 ke kara kai hare-hare, rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) ta yi nasarar karɓar...

Ƴan majalisar wakilai sun rage albashinsu da kaso 50

Mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun amince su rage albashinsu da kaso 50  na tsawon watanni 6 a matsayin nasu sadaukarwar da kuma nuna...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

An kama ɗan sanda kan zargin aikata fashi da makami

Wani jami'in ɗan sanda mai suna Aminu Muhammad dake aiki da rundunar ƴan sandan jihar Kogi ya faɗa komar abokan aikinsa ƴan sanda kan...