Wani mai safarar tabar wiwi ya fada hannun yan sanda a Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wani matashi da yayi safarar ganyen tabar wiwi daga jihar Edo zuwa jihare.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kiyawa ya ce jami’an rundunar na kar ta kwana karkashin jagorancin, CSP Hassan Nasir Jega su ne suka samu nasarar cafke mutumin a Garin Kwanar Dangora dake iyaka da jihar Kaduna, a karamar hukumar Kiru ta jihar.

Ya ce mutumin mai suna Agbor Victor dan shekara 30 ya ce yayi dakon tabar ne da darajarta ta haura miliyan daya domin kai wa wani Alhaji a cikin Kano, wanda tuni ya ranta a nakare

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) Æ™arÆ™ashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da Æ™arar da É—an majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]