Tinubu ya amince da naÉ—in sabon shugaban kwastom

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Adewale Adeniyi a matsayin babban Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Najeriya.

Daraktan yada labarai ga sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, nadin zai fara aiki ne daga ranar 19 ga Oktoba, 2023, kuma wa’adinsa ya biyo bayan wasu tanadin dokokin ma’aikatan gwamnati (PSR).

Idan ba a manta ba, a watan Yuni ne Tinubu ya nada Adeniyi a matsayin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) don maye gurbin tsohon CG, Hammed Ali.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu É—aliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karÉ“ar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...