Connect with us

Hausa

Takaitattun labarai: ‘Yan Shi’a sun shiga hannu; Jirgi ya fadi a Nijar

Published

on

Wasu mata 'yan Shi'a yayin da suke zang-zanga

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

‘Yan Najeriya na ciki da wajen kasar sun shaida abubuwa da dama da suka faru ko dai a cikin kasar ko kuma a makwabta a makon da ya gabata.

Ga wasu abubuwa shida da suka faru a Najeriya ko kuma ga ‘ya’yanta a wasu kasashen:

1- Arangamar ‘yan Shi’a da ‘yan sanda

A ranar Talata ‘yan kungiyar Islamic Movement of Nigeria wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a suka gwabza da ‘yan sanda a Abuja, inda ‘yan sandan suka ce “an harbi” jami’ansu guda biyu.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Anjuguri Manzah, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mabiya Shi’ar sun yi kokarin shiga ginin majalisar dokoki ne da karfin tuwo, inda jami’an ‘yan sanda suka yi kokarin hana su.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Muryar Muhammad Ibrahim Gamawa

Ya kuma ce sun kama mutum 40 wadanda ake zargi da aikata hakan.

Ita kuwa kungiyar, ta bakin Muhammad Ibrahim Gamawa mai magana da yaunta, cewa take ba ta da makaman da ‘yan sandan suka ce ‘ya’yanta sun yi harbi da su.

Ya kara da cewa “mutum 100 ne aka kama ‘yan kungiyar tasu” ba 40 ba kamar yadda ‘yan sanda suka fada.

Za ku iya kallon hotunan barnar da arangamar ta haifar a nan:

2- AFCON 2019: Super Eagles ta kai wasan kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Chukwueze ne dan wasan da ya fi kowanne kokari a wasan

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta kai wasan kusa da na karshe a gasar Cin Kofin nahiyar Afirka da ake yi a Masar, bayan da ta doke Afirka ta Kudu 2-1 a ranar Laraba.

Super Eagles ta fara jefa kwallo a minti na 27 ta hannun Samuel Chukwueze, kafin daga bisani Bongani Zungu ya farke a minti na 71. A minti na 89 ne kuma William Ekong ya kara kwallo ta biyu.

Najeriya za ta kara da Aljeriya ranar Lahadi a matakin kusa da karshe wato Semi Finals a birnin Alkahira.

3- Mutum 11 sun mutu a Nijar

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A kalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu ranar Laraba wasu bakwai kuma suka bata a wani hatsarin jirgin kwale-kwale a gulbin Tibirin Gobir kusa da jihar Maradi.

Wani jirgin ruwa ne dauke da mutane kusan 40 ya nutse yayin da suke neman ketara gulbin daga gaba daya zuwa daya gabar.

Gwamnan jihar Maradi Zakari Umaro ya ce “A yanzu an tsamo mutum 14 amma uku ba su mutu ba, sannan ana ci gaba da neman sauran mutane a cikin ruwan.

4- Buba Galadima ya bayyana a kotu

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Buba Galadima ya bayyana cewa har yanzu fa shi dan jam’iyya mai mulki ne ta APC

Injiniya Buba Galadima, wanda shi ne shugaban tsagin jam’iyyar APC da ake kira rAPC ya bayyana a kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa domin ba da shaida, a ranar Litinin.

A harabar kotun kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Buba Galadima ya ce “‘yarsa ta fi kowanne minista a gwamnatin Buhari ilimi da cancanta” bayan da lauyan APC ya tambaye shi ko yana sane da kasancewar ‘yar tasa a gwamnatin.

Sannan kuma ya shaida wa BBC cewa har yanzu dan jam’iyyar APC ne kuma “babu wanda ya isa ya kore shi daga jam’iyyar”.

5- Mutum biyar da arzikinsu ya fi kasafin kudin Najeriya

Hakkin mallakar hoto
YOUTUBE/MO IBRAHIM FAOUNDATION

Image caption

Aliko Dangote ne mafi arziki a nahiyar Afirka kuma dan Najeriya ne

Rahoton kungiyar agaji ta Oxform wanda ta fitar a ranar Litinin ya ce akwai mutum biyar a Najeriya wadanda arzikinsu ya yi wa kasafin kudin kasar shal.

Arzikin nasu wanda ya kai dala biliyan 29.9, ya zarce naira tiriliyan 7.29 wanda shi ne kasafin kudin na 2017 – kwatankwacin dala biliyan 23.97.

Jaridar Forbes ta wallafa sunayen mutum biyar ‘yan Najeriyar da suka fi arziki a kasar kamar haka:

  • Aliko Dangote
  • Mike Adenuga
  • Abdul Samad Rabiu
  • Folorunsho Alakija
  • Femi Otedola

6- An haramta sayar da Sniper

Hakkin mallakar hoto
TWITTER/@NAFDACAGENCY

Image caption

An bai wa masu hada magungunan da masu sayar da shi wata biyu su kawar da su daga kasuwanni

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya NAFDAC, ta sanar da hana sayar da maganin kashe kwari mai suna Sniper daga kasuwanni da shaguna a fadin kasar.

NAFDAC ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis inda ta kara da cewa haramcin zai hada da yi da kuma shigo da duk magani mai dauke da sinadarin Dichlorvos cikin kasar.

Haramcin na baya-bayan nan ya shafi Sniper da sauran magungunan da ake yi wa shuka feshi da suka hada da Tankill da Gladiator Liquid da Executor Liquid da Smash Super Liquid da DD Force da Glovan da Philopest da Wonder Liquid da Rid-Off da NOPEST da kuma SUMODDVP.

Wannan dai ya biyo bayan labarin yadda maganin na Sniper ya kashe wata ‘yar bautar kasa a jihar Ogun bayan da ta yi amfani da shi a ka domin kashe kwarkwata.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

‘Yan ciranin da suka makale sun bar wani tsibirin Italiya

Published

on

stranded

Kusan ‘yan cirani 100 da ke kan wani jirgin ruwa na jin kai wanda ya makale a tsibirin Lampedusa sun bar tsibirin na Italiya, bayan wani mai shigar da kara ya umarci jirgin ruwan da ya bar tsibirin.

Lokacin da jirgin ya isa tsibirin dai, mutane sun yi musu maraba a yayin da suka dinga sowar “sannu da zuwa” musamman ma ga ‘yan ciranin Afirka.

Mai shigar da kara, Luigi Patronaggio ya umarci da a kwace jirgin wanda mallakin wata kungiyar agaji mai suna Open Arms ne.

Kungiyar ta ce ‘yan ci ranin za su iya fara samun kulawar likitoci, duk da gwamnatin Italiya ta jima tana hana su shiga kasar.

Kafin mai shigar da karar ya yanke hukuncinsa, Sipaniya wadda ita ce gida ga kungiyar ta Open Arms ta aika wani jirgin ruwa zuwa Lampedusa domin ya dauko ‘yan ci ranin.

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

Hukuma ta sake kama rikakken mai satar mutanen nan

Published

on

Yanzu haka masana da kwararru a Najeriya sun yaba wa ‘yan sanda a kan namijin kokari da suka yi wurin zakulo mutumin, suna cewa wannan na nuna lalle fa ‘yan sandan Najeriya jajirtatttu ne.

Masanin Halayyar bil’adama da harkar tsaro, Farfesa Mohammed Tukur Baba ya ce wannan na nuna irin sabon babi da ‘yan sandan suka bude a sha’anin tsaro, duba da irin bajintar da suke ta nunawa da ba ayi tsammani ba, a don haka matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta ba wai ya gagari ‘yan sanda ba ne.

Farfesa Baba ya kara da cewa matakai da suke bi su kamo irin wadannan manyan yan ta’adda ya nuna cewa in sun dukufa kuma suka samu goyon bayan jama’a to fa lalle ‘yan sandan zasu magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Kamo irin wannan babban dan ta’addan inji masanin ka iya aikewa da sako ga duk masu son tafka aika aika, don hakan ya fara bada tsoro cewa lalle komai nisan jifa kasa zai fado, don kuwa dan sandan Najeriya ba kanwan lasa bane.

Lauyan nan mai fafutuka Barrister Yakubu Sale Bawa yace shi tuni yana da kwarin gwiwar lalle ‘yan sandan zasu sake cafke shi Wadumen, duba da cewar lalle ‘yan sandan Najeriya in zasu yi aiki zasu yi, kuma cafke wannan Wadumen zai fito da dalla dallan me ya faru.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Ina Neymar, Eriksen, Varane, Vorm, Mustafi, Ibe, Bravo za su tafi? | BBC Sport

Published

on

Neymar

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Juventus ta fara farautar Neymar

Barcelona na shirin karbar aron Neymar mai shekara 27 daga Paris St-Germain a wannan makon da nufin sayen dan wasan idan an sake bude kasuwar musayar ‘yan wasa. (ESPN)

Juventus ta shiga sahun manyan kungiyoyin da ke bukatar Neymar, inda ta fara tattaunawa da PSG domin karbar dan wasan na Brazil. (AS)

Barcelona ba ta shirya yin watsi da burin dawo da Neymar ba a Camp Nou. (Marca).

PSG ta fi son ta ba Real Madrid Neymar don ta karbi dan wasan baya na Faransa Raphael Varane, mai shekara 26, da kuma matashin dan wasa Vinicius Jr. (Telefoot, via Sun)

Dan wasan Tottenham na Denmark Christian Eriksen, mai shekara 27, ya ce yana sha’awar komawa Barcelona ko Real Madrid ko Juventus. (ESPN)

Arsenal za ta bar dan wasan Jamus Shkodran Mustafi, mai shekara 27 ya koma Roma a matsayin dan wasan aro amma da nufin sayar da shi kan fam miliyan £23m. (Forza Roma, via Sun)

Golan Chile Claudio Bravo, mai shekara 36 zai bar Manchester City a karshen kaka. (Sun)

Ole Gunnar Solskjaer ya nanata cewa Paul Pogba, mai shekara 26, ba zai bar Manchester United ba. (Sky Sports)

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: